Isa ga babban shafi
wasanni

FIFA na gudanar da bincike kan Ingila

Hukumar Kwallon Kafar Duniya wato FIFA na gudanar da bincike kan wake-waken da ake kallo a matsayin na nuna wariya da magoya bayan Ingila suka yi ta rerawa a yayin fafatawar kasar da Croatia a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Croatia ta casa Ingila da ci 2-1 a wasan dab da na karshe a gasar cin kofin duniya a Rasha
Croatia ta casa Ingila da ci 2-1 a wasan dab da na karshe a gasar cin kofin duniya a Rasha 路透社
Talla

Kawo yanzu babu cikakken bayani game da zargin da ake yi wa magoya bayan tawagar ta Ingila da suka rere wannan waka.

Sai dai FIFA ta tabbatar cewa, an shigar da kara game da wakar ta nuna wariya a gabanta kuma tuni ta fara bincike kan lamarin.

Ko a ranar Laraba da ta gabata sai da FIFA ta ci tarar Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila Pam dubu 50 saboda ‘yan wasan kasar da suka hada da Dele Alli da Eric Dier da kuma Raheem Sterling sun sanya wata safar kafa da FIFA ba ta amince da ita ba.

A bangare guda, dan wasan Croatia Luka Modric ya ce, manazarta kan kwallon kafa a Birtaniya sun rena tawagar Croatia gabanin wannan fafatawa da suka tashi 2-1.

Modric ya ce, sun samu kwarin guiwa ne daga kalaman da mutane ke ta furtawa na cewa, ‘yan wasan Croatia sun galabaita saboda wasanni biyu da suka buga da suka kai su ga bugun fanariti.

Modric ya ce, yanzu sun nunawa duniya cewa, lallai ba su gaji ba.

A karon farko kenan a tarihi da Croatia ke kaiwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.