Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 21/02 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 21/02 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 21/02 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 21/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/02 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/02 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 21/02 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 21/02 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 21/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Wasanni

Croatia ta tsallaka wasan karshe a gasar kofin duniya

media Luka Modric da Dejan Lovren na Croatia na murnar samun nasara REUTERS/Kai Pfaffenbach

Kasar Croatia ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha bayan ta doke Ingila da kwallaye 2-1.

Yanzu haka Croatia wadda a karon farko kenan da take samun gurbi a wannan mataki, za ta kece raini da Faransa a wasan karshe a ranar Lahadi.

Kasashen biyu sun fara shafe tsawon mintina 90 suna kan kunnen doki 1-1, lamarin da ya sa aka kara musu lokaci, yayin da Croatia ta kara kwallo ta biyu ta hannun Mario Mandzukic.

Ingila ce ta fara zura kwallo a minti na 5 da saka wasan ta hannun Kieran Trippier, amma Ivan Perisic ya farke a minti na 68.

Tarihi ya nuna cewa, a can baya, kasashen biyu sun hadu sau daya a wata babbar gasa, in da Ingila ta samu nasara da ci 4-2 a matakin rukuni a shekarar 2004 a gasar cin kofin kasashen Turai.

Amma a jumulce, sun hadu sau takwas, in da Ingila ta samu nasara a wasanni hudu ,Croatia ta samu nasara a wasanni uku, sannan suka tashi canjarasa a wasa guda.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure