Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan wasan Colombia na fuskantar barazanar kisan gilla

Jami’an tsaron Colombia sun ce wasu ‘yan kwallon kafa na kasar guda biyu na fuskantar barazanar yi musu kisan gilla, sa’o’i bayan da suka zubar da damar zura kwallaye a ragar Ingila, yayin bugun daga kai sai mai tsaron gida, a gasar cin kofin duniya.

Mai horar da Colombia Jose Pekerman tare da takwaransa na Ingila Gareth Southgate yayin rarrashin daya daga cikin 'yan wasan Colombia da suka barar da damar zura kwallo Mateus Uribe a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Mai horar da Colombia Jose Pekerman tare da takwaransa na Ingila Gareth Southgate yayin rarrashin daya daga cikin 'yan wasan Colombia da suka barar da damar zura kwallo Mateus Uribe a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Carl Recine/Reuters
Talla

Gazawar ta ‘yan wasan Colombia, Mateus Uribe da Carlos Bacca ce ta bai wa Ingila damar kai wa ga zagayen gaf da na kusa da karshe, wato kwata final.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun a birnin Moscow wasu magoya bayan Colombia suka soma furta kalaman cin zarafi da barazana ga ‘yan wasan biyu, mintuna bayan bugun daga kai sai mai tsaron gidan, biyo bayan kammala wasa da suka yi 1-1 harda karin lokaci.

Lamarin dai ya zo ne kwana guda bayan da akai bikin tunawa da wani tsohon dan wasan kwallon kafar Colombia, Andres Escobar, wanda aka yiwa kisan gilla a kasar.

A shekarar 1994 aka bindige Escobar har lahira, sakamakon kuskuren jefa kwallo a ragar kasarsa da ya yi, yayin wasan gasar cin kofin duniya wanda Amurka ta karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.