Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta sauya salon zabar gwarzon dan kwallon kafa na duniya

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce daga yanzu, za’a rika zabar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya na shekarar da muke ciki, daga cikin jerin ‘yan wasa 10, a maimakon yadda ta saba yi na zaben gwarzon dan kwallon kafar daga cikin shahararrun ‘yan wasa 23.

Wani sashi na harabar hedikwatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a birnin Zurich, na kasar Switzerland.
Wani sashi na harabar hedikwatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a birnin Zurich, na kasar Switzerland. REUTERS/Arnd Wiegmann/Files
Talla

Hukumar ta FIFA ta ce kwamitinta mai mambobi 13 ne zai yi aikin tantancewar ko zaben ‘yan wasan 10, kuma daga cikin tsaffin gwarzayen ‘yan wasan kwallon kafar da zasu kasance cikin kwamitin akwai, Ronald Nazario na Brazil da kuma Lothar Matthaus na kasar Jamus.

Ana sa ran a ranar 23 ga watan Yuli da muke ciki, zuwa 10 ga watan Agusta mai zuwa kaftin-kaftin na tawagogin kwallon kafar kasashe, masu horarwa, wasu daga cikin ‘yan jaridu da kuma magoya baya ko masu kallo, zasu kada kuri’ar zabar gwarzon dan kwallon kafa na shekarar 2018.

A ranar 24 ga watan Satumba mai zuwa hukumar FIFA za ta jagoranci bikin karrama dan wasan da ya yi nasarar zama gwani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.