Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta musanta jita-jitar sayen Neymar

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ya musanta batun da ke cewa yana shirye-shiryen sayen dan wasan gaba na PSG kuma mafi tsada a duniya Neymar Junior.

Real Madrid ta ce ba ta yi wata Magana da dan wasan ko kuma Club din na PSG ba.
Real Madrid ta ce ba ta yi wata Magana da dan wasan ko kuma Club din na PSG ba. REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce babu wani shiri a kasa game da tunanin sayo dan wasan wanda PSG ta sayo daga Barcelona kakar da ta gabata kan yuro miliyan 200.

Haka zalika, Madrid ta ce bata yi wata Magana da dan wasan ko kuma Club din na PSG ba.

Wata kafar yada labarai a Spain dai ta yi ikirarin cewa, Madrid din na gab da sayen Neymar kan Yuro miliyan 310 kudi mafi yawa da wata kungiya ta taba taya dan wasa a tarihin cinikayyar ‘yan wasa.

Kawo yanzu dai Neymar ya zura akalla kwallaye 28 a wasanni 30 kacal da ya bugawa PSG tun bayan komawarsa sakamakon jinyar da ya yi ta fama da ita a kakar wasannin da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.