Sabon raunin da Neymar ya samu ya tayar da hankalin 'yan Brazil
Dan wasan gaba na Brazil Neymar, ya fice daga filin da suke asataye a jiya Talata yana dingishi, abinda ya tayar da hankalin tawagar kwallon kafar kasar, da ke shirin tunkarar wasanta da Costarica a ranar Juma’a mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Kakakin hukumar kwallon kafa ta Brazil, Vinicius Rodrigues, ya tabbatar da cewa Neymar ya fice daga filin atasyen ne sakamakon ciwo da zogi da yake ji a idon sawunsa na kafar dama.
Rodriguez ya ce, jerin ketar da ‘yan wasan Switzerland suka rika yi wa Neymar wasan da suka 1-1 da Brazil ne ya janyo wa dan wasan samun raunin.
Kakakin hukumar kwallon ta Brazil, ya kara da cewa, raunin da Neymar ya samu, ba a wurin da ya karya kasusuwan kafarsa a watan Fabarairu, ya sake samu ba, raunin da ya tilasta masa hutun sama da watanni 3.
Ana sa ran a gobe Alhamis Neymar zai fito atasaye, kafin daga bisani su tafi zuwa birnin Saint Petersburg, domin fafatawa da Costarica a ranar Juma’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu