Morocco na gab da ficewa daga gasar cin kofin duniya
A zagaye na biyu na wasannin gasar cin kofin duniya da ke ci gaba da gudana a Rasha Portugal ta lallasa Morocco da ci daya mai ban haushi a wasan daya gudana yau tsakaninsu wanda shi ne was anta na biyu bayan fara gasar.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka dai wasa daya ya ragewa Moroccon wanda kuma matukar ba ta yi nasara ba za ta tattara yanata-yanata ta bar Rashan.
Tun farko Iran ce ta lallasa Moroccon da ci 1 mai ban haushi a zagayen fark gashi yau kuma Portugal ta kara yi mata makamancinsa.
Kasar da ta ragewa Moroccon ita ce Spain a zagaye na 3 kenan wadda kuma ana ganin abu ne mai wuya ta iya doke ta ganin irin bajintar da ‘yan wasan na Spain suka nuna yayin karawarsu da Portugal a zagaye na farko inda suka tashi ci 3-3.
Sau daya Moroccon ta taba yin gagarumar nasara a kan Portugal a tarihin gasar cin kofin duniyar shi ne a shekarar 1986, inda ta lallasa ta da ci 3 da 1 a zagaye na farko ta kara lallasata a zagaye na biyu yayinda suka yi canjaras a zagaye na 3.
Kuma ita Portugal rabon da wata kasa da ba ta Turai ba ta yi nasara akanta tun a shekarar 2002, inda ko a shekarar 2014 gasar cin kofin duniya da ta gudana kenan, wasa 1 ta yi rashin nasara akansa cikin wasanni 10 da ta fafata a gasar, kuma shi ne wanda Jamus ta doke ta ta kuma lashe kofin na 2014.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu