Isa ga babban shafi

Federer ya koma matsayi na 1 a fagen kwallon tennis

Rogder Federar ya samu nasarar komawa matsayinsa na lamba daya mafi kwarewa a fagen wasan kwallon Tennis ajin maza a duniya, bayan da ya lashe kofin gasar Mrecedes a aka kammala jiya a birnin Stuttgart na Jamus.

Roger Federer dan kasar Switzerland.
Roger Federer dan kasar Switzerland. AFP
Talla

Federar dan kasar Switzerland, ya samu nasara a wasan karshen gasar ce, bayan lallasa Milos Raonic dan kasar Canada, da kwallaye 6-4, da kuma 7-6.

Karo na 98 kenan Rodger Federer ke lashe kofunan gasar kwallon Tennis Daban daban.

A halin yanzu Federer ya kafa tarihin zama dan wasan Tennis a biyu a duniya da yafi takwarorinsa yawan lashe kofunan wasannin Tennis, bayan Jimmy Connors dan kasar Amurka da ya lashe kofunan gasar tennis har sau 109, a tsawon lokacin da ya shafe a fagen wasan na tennis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.