Isa ga babban shafi
wasanni

Rasha ta lallasa Saudiyya da ci 5 da nema

Rasha mai masaukin baki ta lallasa Saudi Arabia da ci 5 da nema a wasan farko na cin kofin duniya da ya fara gudana yau din nan. Kafin yanzu dai akwai hasashen cewa Rashan ba lallai ta yi abin kirki a wasan ba, amma daga bisani aka samu juyawar al'amura inda suka lallasa takwarar ta su.

Yanzu haka dai Rashan za ta fuskanci ko dai Masar ko kuma Uruguay a wasan ta na gaba na cin kofin duniyar.
Yanzu haka dai Rashan za ta fuskanci ko dai Masar ko kuma Uruguay a wasan ta na gaba na cin kofin duniyar. REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Tun kafin tafiya hutun rabin lokaci Rashan ta zura kwallaye biyu a ragar Saudi Arabia kuma Lury Gazinsky ne ya zura kwallon cikin mintuna na 12 da fara karawar a filin wasa na Luzhniki da ke birnin Moscow.

Yanzu haka dai Rashan za ta fuskanci ko dai Masar ko kuma Uruguay a wasan ta na gaba na cin kofin duniyar.

Matukar dai Masar ta yi nasara kan Uruguay to ita za ta kara da Rasha haka zalika idan Uruguay ce ta yi nasara itama za ta fuskanci Rashan.

Wasan dai na yau ya samu halartar shugaban kasar Rasah Vladimir Putin da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA baya ga mashahuran mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.