Gasar da za ta shafe kwanaki 32 tana gudana, za a buga wasanni 64 ne, kamar yadda aka sani a tsakanin kasashe 32.
Ana sa rana masu kallo miliyan daya da rabi ne suka hallara a Rasha domin bai wa idanunsu abinci, yayin wannan gasa, yayin da kuma a gefe guda, jami’ai sukai hasashen cewa sama da masu kallo ta kafar talabijin biliyan uku ne zasu bibiyi wasannin daga inda suke.
Brazil ita ce kasa daya tilo da take samun nasarar halartar kowace gasar cin kofin duniya, ko da yake basu samu nasarar lashe kofin gasar ba tun bayan shekarar 2002.