Isa ga babban shafi
wasanni

babu matsala tattare da tawagar Ingila a Rasha - Mourinho

Kociyan Manchester United Jose Maourinho ya ce yana da yakinin cewa tawagar Ingila da ta tafi Rasha za ta kai labari a ilahirin wasannin da za ta doka.Kalaman Mourinho na zuwa ne a dai dai lokacin da jita-jita ke kara yawaita game da rashin gogewar tawagar da Ingila ta tura Rasha.

Mourinho wanda ya bayyana kasashen Brazil da Jamus a matsayin wadanda suka fi hada tawaga mai kyau, amma y ace tawaga mai kyau ba ita ke nuna cewa dole su za su yi nasara ba.
Mourinho wanda ya bayyana kasashen Brazil da Jamus a matsayin wadanda suka fi hada tawaga mai kyau, amma y ace tawaga mai kyau ba ita ke nuna cewa dole su za su yi nasara ba. Reuters/Robert Pratta
Talla

Akwai fargabar cewa hukumar kwallon kafar ta Ingila ta yi ragon azanci wajen aikewa da kananan yara zuwa Rashan wadanda galibinsu basu da gogewar irin gasar hasalima dai dai kune suka taba doka gasar cin kofin duniya.

Sai dai Mourinho ya ce duk da cewa yara aka tura amma dukkaninsu suna da gogewar da ake bukata don kuwa kowannensu na taka leda a manyan kungiyoyin kwallon kafa daban-daban dama na Firimiyar Ingila.

Mourinho wanda ya bayyana kasashen Brazil da Jamus a matsayin wadanda suka fi hada tawaga mai kyau, amma y ace tawaga mai kyau ba ita ke nuna cewa dole su za su yi nasara ba.

Ingila wadda ke a rukunin G za ta fara karawa ne da Tunisia idan ta yi nasara kuma ta kara da guda cikin Belgium ko kuma Panama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.