Isa ga babban shafi
Wasanni

Thiem na gaf da kafa tarihi a gasar Roland Garros

Dominic Thiem dan kasar Australia, kuma dan wasan tennis na 7 mafi kwarewa a duniya ajin maza, ya samu nasarar kai wa wasan karshe na gasar Roland Garros ko French Open da ke gudana a Faransa.

Gasar Rpland Garros: Dominic Thiem dan kasar Austria.
Gasar Rpland Garros: Dominic Thiem dan kasar Austria. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Thiem ya samu nasarar ce, bayan lallasa Marco Cecchinato (Chekinato) na kasar Italia a fafatawar da suka yi dazu,a zayagen wasan kusa da na karshe, inda ya lallasa shi da kwallaye 7-5,7-6, dakuma 6-1.

Karo na farko kenan a tarihin Thiem dan Australia, da ya kai wasan karshe a dukkanin wasannin Grandslam da ya taba shiga a baya, wato wassannin da suka hada da, French Open ko Roland Garros, Australian Open, US Open da kuma Wimbledon.

A halin yazo Thiem zai jira wanda zai yi nasara ne tsakanin Rafeal Nadal dan kasar Spain ko Juan Martin del Potro na Argentina, domin fafatawa da shi a wasan karshe ranar Lahadi mai zuwa.

A bangaren mata kuwa a gasar kwallon tennis din ta Roland Garros da ke gudana a Faransa, Simona Halep ‘yar kasar Romania, kuma lamba 1 a tsakanin takwarorinta na duniya, ta kai wasan karshe, bayan da ta lallasa takwararta ‘yar kasar Spain, garbine Muguruza a wasan kusa da na karshe.

Halep ta samu nasara ne da kwallaye 6-1 da kuma 6-4 akan Muguruza wadda ke rike da matsayin yar kwallon tennis din ta 3 a duniya.

A ranar Asabar mai zuwa Halep zata fafata wasan karshe da Sloane Stephens, bayan da itama Sloane Stephenes mai rike da kofin gasar US Open ta lallasa Madison Keys itama ‘yar kasar Amurka, da kwallaye 6-4 da kuma 6-4 a wasan kusa da na karshe da suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.