Isa ga babban shafi
Wasanni

Fasahar taimakawa alkalin wasa da bidiyo za ta soma aiki a bana

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta ce za a fara amfani da fasahar taimakawa alkalin wasa da hoton bidiyo a gasar cin kofin duniya da za a fara mako mai kamawa a Rasha, karon farko a hukumance, ba a matsayin gwaji ba.

Fasahar amfani da bidiyo wajen taimakawa alkalin wasa.
Fasahar amfani da bidiyo wajen taimakawa alkalin wasa. FIFA.com
Talla

Hukumar FIFA, ta yanke hukuncin ne, bayan kammala nazari, da kuma daukar matakai na gwajin fasahar maimacin bidiyon a wurare daban-daban, da suka hada da gasar Seria A ta kasar Italiya, da kuma gasar Bundesliga ta Jamus.

FIFA ta ce za a yi amfani da fasahar maimacin hoton bidiyon ne a lokutan da suka hada da, bayan an zura kwallo da ake da shakku akanta, lokutan bayar da jan kati, ko kuma idan ta bayyana cewa alkalin wasa yayi kuskuren baiwa dan wasa kati mai dorawa, koma ya kore shi daga fili.

Alkalan wasa 13 ne za su rika aikin lura fasahar ta taimakawa alkalin wasa da maimacin bidiyon, yayin da lokaci zuwa lokaci za a rika sauya alkalan wasan da sauran takwarorinsu 35 da zasu aikin busa wasannin gasar cin kofin duniyar a filli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.