Buhari ya gana da Super Eagles kan gasar kofin duniya
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa tawagar kwallon kafar kasar, wato Super Eagles cewa, nauyin farin ciki ko kuma bakin cikin ‘yan kasar da yawansu ya haura miliyan 180 ya rataya a kanta a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Wallafawa ranar:
Shugaba Buhari wanda ya gana da ‘yan wasan na Super Eagles a yau gabanin tafiyarsu zuwa Rasha don wakiltan kasar ya ce, babu abin da ke hada kan ‘yan kasar kamar wasan kwallon kafa.
Buhari ya bukaci tawagar ta Super Eagles da ta buga wasa cikin tsanaki da kuma lashe kofin duniyar.
A bangare guda, tawagar ta Super Eagles ta rage yawan sunayen 'yan wasan da za su wakilce ta Rasha daga 30 zuwa 25
Kocin tawagar Gernot Rohr ya shaida wa Stephen Eze da Dele Ajiboye da Junior Lokosa da Uche Agbo cewa ba za a bukace su a Rasha ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu