Isa ga babban shafi
Wasanni

Wenger zai yanke shawara kan makomarsa a watan Yuni

Tsohon mai horar da kungiyar Arsenal Arsene Wenger, ya ce a ranar 14 ga watan Yuni mai zuwa, zai bayyana mataki na gaba da zai dauka, dangane da ko zai ci gaba da aikinsa na horarwa tare da wata kungiyar, ko kuma zai karkata zuwa aiki a wani mukamin.

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger.
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger. Reuters/Scott Heppell
Talla

A kakar wasa ta bara ne dai matsin lamba ya karu ga Wenger kan ya ajiye aikinsa, bayan da ya gaza jagorantar Arsenal zuwa gasar zakarun turai.

Zalika a kakar wasa ta bana ma abinda ya faru ne ya sake maimaita kansa, bayanda Arsenal din ta kammala wasanninta a matsayi na 6 a gasar Premier, tabbacin ba za ta samu halartar gasar cin kofin zakarun Nahiyar turai mai zuwa ba.

Kafin ajiye aikin nasa, an rawaito cewa akwai yiwuwar Arsene Wenger ya koma horar da kungiyar Paris saint-Germain sai kuma a baya bayan nan da aka rawaito cewa mai yuwuwa Wenger ya koma horar da kungiyar Monaco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.