Isa ga babban shafi
Wasanni- Rasha

Rasha zata girke na'urori don tabbatar da tsaro a filayen wasanni

Rasha zata girke na’urori a filayen da za a buga wasannin gasar cin kofin duniya, irin wadanda da aka yi amfani da su a yake-yaken kasashen Syria da Ukraine, don kare filayen daga yiwuwar kai hare-haren ta’addanci musamman ta hanyar amfani da jirage marasa matuki ko mai layar zana.

Wani jirgi maras matuki yayin gwajin amfani da shi wajen leken asirin sha'anin tsaro da ayyukan ceto a birnin Zurich na kasar Switzerland. 23, Augusta, 2017.
Wani jirgi maras matuki yayin gwajin amfani da shi wajen leken asirin sha'anin tsaro da ayyukan ceto a birnin Zurich na kasar Switzerland. 23, Augusta, 2017. ©Fabrice COFFRINI / AFP
Talla

Batun samar da cikakken tsaro dai shi ne kan gaba wajen masu shirya yadda gasar cin kofin duniyar zata gudana a kasar ta Rasha daga 14 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuli.

Rasha ta fuskanci wasu hare-haren kunar bakin wake tun bayan da ta yi nasarar samun damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniyar ta bana a shekarar 2010, hare-haren da ta dora alhakinsu kan wasu kungiyoyin mayaka da ke arewacin kasar masu alaka da kungiyar IS.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce amfani da na’urorin ba zai tsaya a filayen wasanni 12 da za a yi amfani da su ba kadai, za a girke na’urorin a dukkanin filayen atasaye da kuma otal ko masaukan da ‘yan wasa na kasashen 32 zasu yi amfani da su, a iya tsawon lokacin da zasu shafe zaune a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.