Isa ga babban shafi
Wasanni

Ana korafi kan tsadar tikitin kallon wasan karshen zakarun turai

Masoya kwallon wasanni su bayyana korafi akan yadda farashin tikitin da shiga kallon wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai, ya yi tsadar gaske a wannan karon.

Wasu magoya bayan kungiyar Liverpool.
Wasu magoya bayan kungiyar Liverpool. Reuters
Talla

Za a buga wasan karshen tsakanin Liverpool da Real Madrid, a filin wasa na Olympic da ke Ukraine.

Wasu magoya bayan kungiyoyin, da ma masoya kallon kwallon kafa, sun koka bisa cewa farashin ya ninka fiye da sau 18 idan aka kwatanta da yadda yake a baya.

A yanzu wadanda ke bukatar samun wurin zama ajin farko a wasan karshen na zakarun turai, tilas su biya Fam 14,000 kamar yadda aka rawaito cewa kungiyar Liverpool ta tsaida farashin akan tikitinta mafi tsada.

Yayinda a bangaren Real Madrid farashin tikitin yake da dan sauki, inda mafi karancinsa yake kan fam 410.

A nata bangaren kuwa kungiyar Liverpool da ta bada odar saida tikitinta 16,626, mafi karancin farashinsa shi ne fam 1,337. Hakan tasa wasu ke zargin kungiyoyini na son amfani da damar wasan karshen ne domin tara kudaden shiga masu yawan gaske.

Filin Olympic da za a buga wasan karshen na gasar cin kofin zakarun turan yana daukar yawan masu kallo 63,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.