Isa ga babban shafi
Wasanni

Buffon ya yi bankwana da Juventus

Mai tsaron raga na Juventus Gianluigi Buffon ya samu kyautuka da karramawar magoya bayan kungiyar, bayan da ya kawo karshen wasa a cikinta a fafatawar da suka yi da Verona.

Mai tsaron raga na Juventus Gianluigi Buffon yayin fita daga wasan karshe da ya bugawa kungiyar.
Mai tsaron raga na Juventus Gianluigi Buffon yayin fita daga wasan karshe da ya bugawa kungiyar. Massimo Pinca/Reuters
Talla

Yayin wasan da Juventus ta lallasa Verona da 2-1, an canza Buffon a mintuna na 63, domin bashi damar ganawa da magoya bayansa, wadanda suka karrama shi ta hanyar mikewa tsaye baki daya.

A shekarar 2001 Buffon ya sauya sheka daga kungiyar Parma zuwa Juventus akan fam miliyan 32, wanda a waccan lokacin ya kafa tarihin zama mai tsaron raga mafi tsada a duniya.

Tuni dai kungiyar Paris St-Germain ta yi wa Buffon tayin buga mata wasa, yayinda a Juventus ta yi masa tayin mukamin zama daga cikin mataimakan masu horarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.