Isa ga babban shafi
wasanni

Levente ta hana Barcelona kafa tarihi a La Liga

Barcelona ta gaza kafa tarihin kammala kakar gasar La Liga  ta bana ba tare da an doke ta ko sau daya ba, bayan Levante ta zazzaga mata kwallaye 5-4 a karawar da suka yi a jiya, lamarin da ya bakanta ran magoya bayan kungiyar a sassan duniya.  

Emmanuel Boateng ya ci wa Levante kwallaye uku a karawar ta jiya
Emmanuel Boateng ya ci wa Levante kwallaye uku a karawar ta jiya REUTERS/Heino Kalis
Talla

Dan wasan Barcelona Philippe Coutinho ya zura kwallaye uku yayin da Luis Suarez ya zura ta hudu a bugun daga kai sai mai tsaren gida, amma hakan bai taimaka wa kungiyar kai wa ga gaci ba.

Emmanuel Boateng ya ci wa Levante  kwallaye uku a karawar ta 37  wadda daga ita sai ta karshe da Barcelonan za ta yi da Real Socidad a makon gobe.

Kocin Barcelona Ernesto Valverde ya hutar da Lionel Messi a wasan na jinya, lamarin da wasu ke ganin cewa ya taimaka wajen kashin da Barcelona ta sha.

Valverde ya ce, sun yi matukar bakin cikin rashin samun nasarar kammala La Liga ba tare da an doke su ba.

A shekarar 1931-32, Real Madrid da ta kasance babbar mai hamayya da Barcelona ta kafa tarihin kammala gasar La Liga ba tare an casa ta ko sau daya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.