Ko Madrid na cikin fargabar rashin Ronaldo a wasanta da Liverpool?
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane, ya ce, akwai yiwuwar gwarzon dan wasansa, Christiano Ronaldo zai murmure gababnin fafatawar karshe da za su yi da Liverpool a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.
Wallafawa ranar:
Ronaldo mai shekaru 33 da haihuwa ya yi rauni a sahun kafarsa a yayin karawar da suka tashi 2-2 da Barcelona a jiya a gasar La Liga ta Spain, kuma nan gaba kadan ne za a dauki hoton sahun nasa.
Ronaldo wanda ya samu raunin a yayin zura kwallo a ragar Barcelona, bai kammala wasan na jiya ba, yayin da aka sauya shi bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Zidane ya ce, ba zai iya bada bayani ba game da tsawon lokacin da Ronaldo zai shafe na jinya amma dai kawo yanzu yana jin jiki.
Zidane ya kara da cewa, ko kadan ba su da wata fargaba game da karawar karshe da za su yi da Liverpool a gasar ta zakarun Turai a ranar 26 ga wannan wata na Mayu a birnin Kiev na Ukraine.
Real Madrid dai na fatan lashe kofin na zakarun Turai karo uku a jere.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu