Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona na gaf da kafa tarihi a gasar La liga

Kungiyar Barcelona ta ci gaba da kare kokarin da take yi na kafa tarihi a gasar La liga na kammala wasaninta ba tare da ta yi rashin nasara ba, bayan da aka tashi 2-2 tsakaninta da abokiyar hamayya Real Madrid Camp Nou.

'Yan wasan kungiyar Barcelona bayan kammala fafatawa da Real Madrid a wasan La liga da aka tashi 2-2.
'Yan wasan kungiyar Barcelona bayan kammala fafatawa da Real Madrid a wasan La liga da aka tashi 2-2. Reuters
Talla

Suarez da Lionel Messi ne suka zurwa Barcelona kwallayenta, yayinda Cristiano Ronaldo da kuma Gareth Bale suka ci wa Madrid nata.

Har yanzu dai akwai ragowar wasanni guda biyu da suka ragewa Barcelona kafin ta tabbatar da kafa sabon tarihin na zama kungiya a gasar La liga ta farko da ta kammala kakar wasa ba tare da an samu nasara akanta ba.

A bangaren ‘yan kungiyar Real Madrid a iya cewa hantarsu ta dan kada yayin wasan bayanda Cristiano Ronaldo ya samu rauni akan idon sawunsa a lokacin da ya zura kwallon farko a ragar Barcelona.

Amma daga bisani mai horar da kungiyar ta Madrid Zinaden Zidane ya bayyana kwarin gwiwar Ronaldo Zai mumure ya kuma samu buga wasan karshe na cin kofin zakarun turai da zasu fafata da Liverpool a ranar 26 ga watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.