Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool zata fafata wasan karshe da Madrid a Kiev

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta samu kaiwa ga buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai inda zata fafata da mai rike da kofin gasar Real Madrid.

Wasu 'yan wasan kungiyar Liverpool yayin murnar kaiwa ga zagayen karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.
Wasu 'yan wasan kungiyar Liverpool yayin murnar kaiwa ga zagayen karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai. John Sibley/Reuters
Talla

A wasan da aka buda rana Laraba Roma ta lallasa Liverpool da kwallaye 4-2, sai dai duk da haka Liverpool ce ta samu kaiwa ga wasan karshe, kasancewar a zahayen farko na wasan kusa dana karshe, Liverpool ce ta lallasa Roma da kwallaye 5-2 a filinta na Anfield da ke Ingila.

Karo na farko kenan da Liverpool ta samu kaiwa ga matakin wasan karshe na gasar zakarun turai, tun bayan shekara ta 2007.

A ranar 26 ga watan Mayu mai zuwa za'a kece raini tsakanin Real Madrid da Liverpool a katafaren filin wasannin Olympics da ke Kiev a kasar Ukraine.

Rabon da kungiyoyin su hadu a irin wannan mataki tun a shekarar 1981, inda Liverpool da samu nasara akan Madrid da 1-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.