Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyar Roma ta koka bisa kura-kuran alkalin wasa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Roma James Pallotta, ya ce tilas ne daga yanzu a fara amfani da fasahar maimaicin hoton bidiyo a gasar zakarun turai, idan akayi la’akari da irin yadda wasu alkalan wasa ke tafka kura-kurai da gangan ko akasin haka.

'Yan wasan kungiyar Roma Patrik Schick da Cengiz cikin damuwa, bayan kammala wasa tsakaninsu da Liverpool a birnin Rome. 2 ga watan Mayu, 2018.
'Yan wasan kungiyar Roma Patrik Schick da Cengiz cikin damuwa, bayan kammala wasa tsakaninsu da Liverpool a birnin Rome. 2 ga watan Mayu, 2018. Reuters
Talla

Pallota ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci akan wasan da kungiyar Liverpool ta samu nasara akan Roma da jimillar kwallaye 7-6, bayan da aka tashi wasan na ranar Laraba Roma na da 4 liverpool kuma 2.

Sai dai a zagayen farko na wasan da suka fafata a ingila Liverpool ce ta lallasa Roa da kwallaye 5-2.

A cewar Pallotta alkalin wasa ya hana kungiyar tasa damar samun bugun daga kai sai mai tsaron gida har sau biyu, wato a lokacin da aka kayar da Edin Dzeko a gidan Liverpool yadi na 16 amma aka ce Dzekon satar fage ya yi.

Pallota ya kuma ce mai tsaron baya na Liverpool Alexander-Arnold ya taba kwallo da hannu a yadi na 16 abinda ya hanawa Roma damar zura wata kwallon, kuma kamata ya yi a basu damar bugun daga kai sai mai tsaron gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.