Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid na gaf da sake kafa sabon tarihi

Real Madrid ta yi nasarar kaiwa ga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun turai karo na uku a jere, kuma karo na 4 cikin shekaru 5, bayan da aka tashi wasa 2-2 tsakaninta da Bayern Munich a Spain.

'Yan wasan Real Madrid tare da sauran manbobin tawagar kungiyar, yayinda suke murnar kaiwa ga wasan zagaye na karshe a gasar cin kofin zakarun turai, bayan wasansu da Bayern Munich.
'Yan wasan Real Madrid tare da sauran manbobin tawagar kungiyar, yayinda suke murnar kaiwa ga wasan zagaye na karshe a gasar cin kofin zakarun turai, bayan wasansu da Bayern Munich. REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Idan har Real Madrid ta samu nasarar lashe kofin zakarun turai na bana, zata sake kafa tarihin zama kungiya ta farko da ta fara lashe kofunan gasar sau uku a jere.

Benzema ne dai ya ciwa Real Madrid dukkanin kwallayenta a wasan na ranar Talata, yayinda James Rodriguez da kuma Joshua Kimmich suka ciwa Bayern Munich nata kwallayen.

Nasarar ta baiwa Madrid damar doke Munich da jimillar kwallaye 4-3, kasancewar a wasan farko da suka fafata, Madrid ce ta yi nasara akanta da kwallaye 2-1 a filin wasa na Allainz Arena da ke Jamus.

Karo na farko da Benzema ya ciwa Madrid kwallaye har biyu a wannan gasa ta zakarun turan, duba da cewa kwallo daya kawai ya ci a wasanni 12 da ya bugawa kungiyar a baya.

Muhimman ‘yan wasan kungiyar Bayern Munich basu samu buga wannan wasa na jiya ba abinda yasa wasu masu sharhin ke ganin na daya daga cikin abinda ya ragewa Byern Munich karsashi, daga cikin yan wasan akwai, Arjen Robben, Jerome Boateng, Arturo Vidal da kuma Manuel Neuer.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.