Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasar zakarun turai: An girke 'yan sanda 3,000 a birnin Rome

Rundunar ‘yan sandan kasar Italiya, ta girke jami’anta akalla dubu 3,000 a birnin Rome, domin samar da cikakken tsaro, yayinda ake shirin fafata wasan kusa dana na karshe zagaye na biyu, tsakanin Liverpool da AS Roma a gasar zakarun turai.

Wasu daga cikin jami'an tsaro da ke sintiri a birnin Rome, Italiya, yayinda ake shirin fafata wasa tsakanin Liverpool da AS Roma.
Wasu daga cikin jami'an tsaro da ke sintiri a birnin Rome, Italiya, yayinda ake shirin fafata wasa tsakanin Liverpool da AS Roma. AFP
Talla

Hukumomin Italiya sun dauki matakin ne, domin fargabar kada a samu arrangama tsakanin tawagar magoya bayan kungiyar Liverpool mai kunshe da magoya baya 5000 da na Roma a filin wasa na Stadio Olimpico.

Zaman dar dar din ya samo asali ne, a makon da ya gabata, bayanda wasu magoya bayan AS Roma, suka jikkata wani magoyin bayan Liverpool Sean Cox mai shekaru 53, a gaf da filin wasa na Anfield a Ingila.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan Birtaniya ma na daga cikin rundunar jami’an tsaron ta Italiya, inda a filin wasan na Stadio Olimipico da za’a fafata ‘yan sanda 1,000 aka girke, sauran 2,000 kuwa zasu yi sintiri ne a titunan birnin na Rome.

Har ila yau duk akan wasan na yau, hukumomin Italiya sun haramta saye ko shan barasa yayin kallon wasan, tare daukar tsauraran matakan zakulo magoyan bayan da zasu yi yunkurin shiga kallon wasan da tikitin Jabu.

A shekarar 1984 magoya bayan Liverpool da dama ne suka jikkata sakamakon suka da wukake, bayan da suka yi tattaki zuwa birnin Rome a wasan karshe na kofin Turai inda suka samu nasara akan kungiyar AS Roma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.