Isa ga babban shafi
Wasanni

Salah zai iya lashe kyautar Ballon d'Or - Wright

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar Arsenal Ian Wright, ya ce akwai yiwuwar Mohammed Salah ya samu nasarar lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Ballon d’Or ta bana.

Dan wasan kungiyar Liverpool Mohammed Salah.
Dan wasan kungiyar Liverpool Mohammed Salah. REUTERS/Andrew Yates
Talla

Wright ya ce Salah zai iya samun wannan nasara muddin ya jagoranci kungiyarsa ta Liverpool wajen lashe kofin gasar zakarun nahiyar turai.

Zuwa yanzu Salah dan kasar Masar, ya ci jimillar kwallaye 43 a wasanni 47 da ya bugawa Liverpool, tun bayan barin tsohuwar kungiyarsa ta Roma.

A cewar Ian Wright baa bun mamaki bane Mohammed Salah ya kawo karshen mamaye kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka yi tun daga shekarar 2008.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.