Isa ga babban shafi
wasanni

Salah ya lashe kyautar gwarzon dan wasa a Ingila

Dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara ta kungiyar kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa a Ingila.

Mohamed Salah na Liverpool
Mohamed Salah na Liverpool REUTERS/Phil Noble
Talla

Salah mai shekaru 25 ya doke Kevin Bruyne da Harry Kane da Leroy Sane da David Silva da David Gea da wajen samun kuri'ar lashe kyautar.

Salah dan asalin Masar ya nuna murnarsa matuka game da wannan kyauta da ya ce, karramawa ce musamman idan aka yi la’akari cewa, ‘yan wasa ne ke kada kuri’ar wanda ya cancaci lashe ta.

Salah dai ya zura kwallaye 31 a wasanni 33 da ya buga a gasar firimiyar Ingila a bana.

Sane na Manchester City ya lashe kyautar gwarzon matashin dan wasa, yayin da Fran Kirby ta Chelsea ta lashe gwarzuwar ‘yar wasa a bangaren mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.