Isa ga babban shafi
wasanni

Mutane 5 ke takarar mukamin Arsen Wenger

Mutane biyar ne ake sa ran dayansu zai gaji kocin Arsenal Arsen Wenger dan kasar Faransa da zai ajiye aikinshi a matsayin mai horas da ‘yan wasar kwallon kafa na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal bayan da ya kwashe shekaru 22 yana jagorantar Club din na Ingila.

Arsenal Wenger took over at Arsenal in 1996 and revolutionised the approach to football in England.
Arsenal Wenger took over at Arsenal in 1996 and revolutionised the approach to football in England. Reuters/Scott Heppell
Talla

Yanzu dai wannan labarin na can ya haifar da jita-jitar shin wai waye zai gaji Arsen Wenger ne, kuma yanzu haka an fara cece-ku-ce akan mutane 5 da ake zaton mai yuwa dai daga cikinsu ne zai gaji wannan Gadon da Wenger ya sauka.

Wadanda ake ta cece-ku-ce akansu dai su ne:

1 - Patrick Vieira (New York City)

2 – Brendan Rodgers (Celtic)

3 - Joachim Loew (Germany

4 - Carlo Ancelotti (unattached)

5 - Luis Enrique (unattached)

Kuma kowanne daga cikin wadannan mutanen da ake zaton ka iya samun damar dare mukamin na Manajan Club din Arsenal, na da kyakkyawan tarihin nasarorin da suka samu a fagen tamola.

To sai dai babban jami’in gudanarwa na Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Ivan Gazidis ya ce hakika yana huskantar babban kalubale na abinda ba zai yiwu ba, wato samun wanda zai maye gurnin Arsen Wenger.

Arsen Wenger dai ya bayyana shirin ajiye mukaminsa ne a kafar sadarwa ta zamani inda ya bayyana cewar bayan da ya tsaya da kyau ya lura da yadda al’amurra ke tafiya a rayuwarsa, ya kuma tattauna da jami’an Club din da yake yi wa aiki, sai ya yanke shawarar cewar lokaci ya yi da ya kamata ya ajiye hakanan ya huta, kuma ya nunawa Club din jin dadinsa da yadda suka bashi damar yi wa Club din aiki shekaru aru-aru.

To bayan bayyana shirin saukar tashi ne aka ce wasu ‘yan wasarsa da suka hada da Tony Adams, da Tierry Henry suka bayyana yadda za su yi kewar Ogan nasu da suka bayyana a matsayin gwarzon tsara karatun tamola na Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.