Isa ga babban shafi
wasanni

'Yan wasan Man City 5 sun shiga jerin da za a fitar da zakaran Firimiya ciki

Wata kungiyar kwarrru da ke kula da ‘yan wasan da suka nuna bajinta a gasar firimiya kowacce shekara ta fitar da sunayen ‘yan wasa 11 wadanda a cikinsu ne za ta fitar da mafi hazaka bana a gasar ta Firimiya.

'Yan wasan Manchester City suna murnar lashe kofin Premier a Ingila.
'Yan wasan Manchester City suna murnar lashe kofin Premier a Ingila. REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Daga cikin ‘yan wasan wadanda 5 daga ciki sun fito daga Manchester city mai rike da kambu.

Cikin ‘yan wasan dai akwai Kyle Walker da Nicolas Otamendi da David Silva da Kevin De Bruyne da kuma Sergio Aguero.

Ita ma dai kungiyar kwallon kafa ta Tottenham na da ‘yan wasa 3 da aka sanya cikin jerin ‘yan wasan mafiya hazaka da suka hadar da Harry Kane.

Sai kuma mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United David de Gea.

Haka zalika akwai dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah, dan wasan da ya kafa tarihi ta hanyar zura kwallaye 40 cikin kaka guda wanda kuma tuni aka sanya sunanshi cikin jerin ‘yan wasan da za a tantance mafi hazaka cikinsu a bana.

Ita kuwa Chelsea na da dan wasa guda ne daya shiga cikin jerin wato Marcos Alonso.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.