Isa ga babban shafi
Wasanni

Ko wacce kungiya ce za ta kai labari a gasar zakarun Turai?

Wallafawa ranar:

Shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da kungiyoyi hudu da za su fafata da juna a matakin wasan dab da na karshe a gasar zakarun nahiyar Turai, in da Real Madrid za ta kece raini da Bayern Munich, yayin da Liverpool za ta kai ruwa rana da Roma. Sai dai masharhanta na ganin cewa, mawuyaci ne Real Madrid mai rike da kambi ba ta fafata da Liverpool a wasan karshe ba. Masu iya magana na cewa, ba a sanin maci tuwo sai miya ta kare.

Ana ganin Real Madrid da Liverpool za su hadu a matakin wasan karshe a gasar ta zakarun Turai
Ana ganin Real Madrid da Liverpool za su hadu a matakin wasan karshe a gasar ta zakarun Turai REUTERS/Stefan Wermuth
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.