Isa ga babban shafi
wasanni

Jami'an FIFA sun isa Morocco kan gasar cin kofin duniya ta 2026

Tawagar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta isa Morocco yau litinin don gudanar da gwaje-gwaje da nufin gano ko kasar ta na da zarafin da za ta iya karbar bakoncin gasar cin kofin duniya na 2026 kamar yadda ta bukata ko a a.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino. REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Tawagar ta mutane 5 za ta shafe kwana 3 ta na aikin, inda a gobe talata za ta ziyarci filayen wasannin kasar da wuraren atisaye baya ga kafofin yada labarai don tabbatar da cewa kasar za ta iya karbar bakoncin dimbin jama’ar a 2026.

Matukar dai FIFAr ba ta samu matsaloli kan yiwuwar karbar bakoncin na Morocco ba, babu shakka kasar za ta zamo guda daya tilo daga nahiyar Afrika da ta taba karbar bakoncin gasar.

Sauran kasashen da suka nuna bukatar karbar bakoncin gasar a 2026 sun hadar da Amurka da Canada da kuma Mexico, ko da yake dai batun Amurka tuni ya fara gamuwa da cikas la’akari da yadda wasu ke ganin akwai karancin tsaro musamman kan abin da ya shafi harbin babu gaira babu dalili.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.