Isa ga babban shafi
Wasanni

United ta fuskanci koma baya irinsa na farko cikin shekaru 60

Sevilla ta fitar da Manchester United daga gasar zakarun nahiyar turai, bayan samun nasarar da ata yi akanta da 2-1 a wasan mataki na kungiyoyi 16, bayan da a wasan farko aka tashi canjaras-0-0.

Dan wasan Manchester United Alexis Sanchez, yana alhinin rashin nasarar da suka yi a hannun Sevilla da 2-1 a filin wasa na Old Trafford, a gasar zakarun turai.
Dan wasan Manchester United Alexis Sanchez, yana alhinin rashin nasarar da suka yi a hannun Sevilla da 2-1 a filin wasa na Old Trafford, a gasar zakarun turai. REUTERS/David Klein
Talla

Dan wasan Sevilla Wissam ben Yedder ne ya zura duka kwallyen biyu, yayinda Romelu Lukaku ya zurawa United kwallo daya tilo da ta ci.

Karo na farko kenan da Manchester United ta gaza kai wa matakin gaf dana kusa da karshe (kwata Final) acikin shekaru 60.

United ta bi sawun kungiyar Tottenham wadda itama kungiyar Juventus ta yi waje da ita a gasar zakarun nahiyar turan.

Manchester City, Liverpool ne suka samu kai wa zagayen Quarter Final, sai kuma Chelsea da ke dakon ko zata samu nasarar lallasa Barcelona a wasan da zasu buga yau a Filin wasa na Nou Camp.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.