Isa ga babban shafi
wasanni

Arsenal za ta maido da martabarta a idon magoya bayanta

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce, dole ne kungiyar ta maido da magoya bayanta don ci gaba da karfafa ma ta gwiwa bayan ‘yan wasansa sun yi nasarar casa Watford da ci 3-0 a gasar firimiya ta Ingila jiya Lahadi duk da cewa dubban magoya bayan sun kaurace wa kallon fafatawar a Emirates.

Arsène Wenger na Arsenal
Arsène Wenger na Arsenal REUTERS/Phil Noble
Talla

Nasarar ta jiya na zuwa ne bayan Arsenal ta sha kashi a wasanni uku da ta yi a jere a gasar ta firimiya, lamarin da ya janyo wa Wenger caccaka daga magoya bayan kungiyar.

Kwallayen da Shkodran Mustafi da Pierre-Emerick Aubameyang da Henrikh Mkhitaryan suka zura sun bai wa Arsenal damar samun nasararta ta farko a gasar tun bayan lallasar da ta yi wa Everton da ci 5-1 a ranar 3 ga watan Fabairu.

Wenger ya ce, babu shakka sun tsinci kansu a cikin tsaka mai wuya da ya ritsa da magoya bayansu, amma za su ci gaba da taka rawa don dadadawa magoya bayansu kamar yadda ya fadi.

A karo na biyu kenan da ake doke Watford a cikin wasanni shida da ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.