Isa ga babban shafi
wasanni

Matic ya cire wa Manchester United kitse a wuta

Dan wasan Manchester United Nemanja Matic ya cire wa kungiyar kitse a wuta, in da ya jefa kwallo ta uku da ta ba ta nasara a karawar da ta shi 3-2 da Crystal Palace a gasar firimiyar Ingila.

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce, suna da kwarin gwiwar samun nasara a wasanninsu
Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya ce, suna da kwarin gwiwar samun nasara a wasanninsu REUTERS/Peter Powell
Talla

Crystal Palace ce dai ta fara zura kwallaye biyu a minti na 11 da kuma 48, amma Smalling da Lukaku suka farke kwallayen biyu a minti na 55 da kuma 76, yayin da Matic ya jefa kwallon karshe a minti na 91, wato dai dai lokacin tashi wasan.

Yanzu haka Manchester United ta dare mataki na biyu a teburin gasar, in da ta ke bin Manchester City mai jan ragama.

Tuni wannan nasarar ta Manchester United ta cilla Crystal Palace matakin ‘yan dagaji.

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce, a koda yaushe yana da yakinin za su rika samun nasara a wasanninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.