Isa ga babban shafi
wasanni

IOC ta janye dakatarwar Rasha kan wasannin Olympics

Hukumar da ke kula da wasannin Olympics ta duniya IOC ta janye dakatarwa da ta yiwa rasha daga shiga wasannin Olympics, bayan dakatarwar baya-bayan nan daga shiga wasannin da ya gudana a Pyeongchan a cikin watan nan.

Tawagar 'yan wasan Olympics na Rasha karakshin Jagorancin Alexander Zubkov a shekarar 2014.
Tawagar 'yan wasan Olympics na Rasha karakshin Jagorancin Alexander Zubkov a shekarar 2014. REUTERS/Issei Kato
Talla

A baya dai IOC din ta ce Rashan ba za ta halarci makamantan wasan ba sakamakon hujjojin da ta ke da su kan yadda ‘yan wasanta ke amfani da kwayoyin kara kuzari.

Sai dai Sanarwar ta IOC a yau, ta ce dukkanin gwaje-gwajen da aka yi kan tawagar ‘yan wasan na Rasha a yanzu ya nuna cewa ba su yi amfani da wasu kwayoyin kara kuzari ba.

Dama dai gabanin karkare gasar wasannin Olympics din a Korea ta kudu ranar Lahadin da ta gaba, hukumar ta IOC ta ce akwai yiwuwar ta janye dakatarwa matukar ba a samu Rashan da karya wata doka ba.

Sanarwar ta IOC ta ce janye dakatarwar za ta fara aiki ne nan ta ke.

Tuni dai shugaban hukumar wasannin Olympics a Rashan Alexander Zhukov ya yi maraba da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.