Isa ga babban shafi
wasanni

Rauni zai hana Neymar karawa da Ronaldo na Madrid

Ga alama gwarzon dan wasan PSG, wato Neymar De Silva ba zai samu damar buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Real Madrid ba a gasar cin kofin zakarun Turai, matakin kungiyoyi 16 zagaye na biyu saboda raunin da ya samu a kafarsa kamar yadda binciken likitoci ya tabbatar.

Neymar ya ci wa PSG kwallaye 29 a wasanni 30 da ya buga ma ta tun bayan da ya raba gari da Barcelona
Neymar ya ci wa PSG kwallaye 29 a wasanni 30 da ya buga ma ta tun bayan da ya raba gari da Barcelona AFP
Talla

Neyma mai shekaru 26 kuma dan asalin kasar Brazil ya gamu da raunin ne a fafatawar da PSG ta doke Marseille da 3-0 a ranar Lahadi a gasar Lig 1 ta Faransa, lamarin da ya sa aka cincibe shi akan gadon daukan mara lafiya cikin hawaye.

Sai dai kawo yanzu, PSG ba ta tabbatar da tsawon kwanakin da zai yi na jinya ba.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi fatan warkewar Neymar cikin hanzari don samun damar fafatawa da ‘yan wasansa da suka hada da Christiano Ronaldo.

PSG ta siyi dan wasan ne daga Barcelona akan farashin Pam miliyan 200 a cikin watan Agustan bara, in da ya ci ma ta kwallaye 29 cikin wasanni 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.