Isa ga babban shafi
wasanni

Na kasa samun barci saboda wasanmu da Barcelona- Conte

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Antonio Conte ya ce, ya gamu da matsalar rashin samun barci a yayin da ‘yan wasansa ke shirin fafatawa da Barcelona a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a Stamford Bridge a yau Talata.

Kocin Chelsea Antonio Conte na cikin tsaka mai wuya saboda rashin karsashin kungiyar a bana
Kocin Chelsea Antonio Conte na cikin tsaka mai wuya saboda rashin karsashin kungiyar a bana REUTERS
Talla

Chelsea ta yi nasarar lashe wasanni hudu daga cikin wasanni 12 da ta buga a baya-bayan nan, yayin da ake ganin Barcelona ka iya doke ta a wasan na yau.

Ko da dai Chelsea ta taba samun nasara akan Barcelona a shekara 2012 kuma a matakin wasan dab da na karshe a gasar zakarun Turai.

Conte ya ce, Barcelona na daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya, kuma akwai yiwuwar ta yi nasara, amma Chelsea za ta samu wata dama ta gwajin matsayinta a karawa da Barcelona kamar yadda Conte ya ce.

Kocin na Chelsea ya sha matsin lambar sauka daga mukaminsa sakamakon rashin karsashin da kungiyar ke nunawa a kakar bana, lamarin da ya sa ake tafka muhawara game da makomarsa a kungiyar.

Ita ma Besiktas za ta ziyarci Allianz Arena a yau don kece raini da Bayern Munich a gasar ta zakarun Turai.

Golan Bayern Munich Manuel Neuer, shi kadai ne ba zai samu damar shiga a fafata da shi a wasan na yau ba saboda jinyar raunin da ya ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.