Infantino zai halarci bikin karrama 'yan wasan Najeriya a yau
Yau ne za a gudanar da gagarumin bikin karrama ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya maza da mata da sauran wadanda suka yi fice a fannin tamaula a bara, bikin da zai samu halartar shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino da shugaban hukumar kwallon kafar Afrika, Ahmad Ahmad.
Wallafawa ranar:
Jihar Legas ce za ta karbi bakwancin bikin karashin jagorancin hukumar kwallon kafar Najeriya, NFF da kuma hadin gwiwar kamfanin AITEO da hukumar CAF.
Daga cikin manyan baki akwai gwamnan Legas AKknwumi Ambode da tsoffin zaratan ‘yan wasan Najeriya irinsu, Austin Jay-Jay Okocha da Kanu Nwankwo da Mutieu Adepoju da Garba Lawal da Daniel Amokachi da Christian Okechukwu da Olusegun Odegbami da sauransu.
A karon farko kenan da hukumar NFF ke shirya irin wannan gagarumin biki don kara wa ‘yan wasan kwallon kafar kasar kwarin gwiwa.
Wadanda za a bai wa lambar yabo sun hada da gwarzon dan wasan shekara na miji da gwarzuwar ‘yar wasa shekara mace da kungiyar da ta fi shara a kakar bara.
Za a watsa bikin kai tsaye a kafar talabijin ta AIT da kuma Super Sport da misalin karfe bakwai na daren yau agogon Najeriya.
JERIN SUNAYEN 'YAN WASAN DA ZA A ZABA A BIKIN NA YAU:
1) GWARZON DAN WASAN SHEKARA NAMIJI
Victor Moses
Wilfred Ndidi
Anthony Okpotu
2) GWARZOWAR 'YAR WASAN SHEKARA MACE
Asisat Oshoala
Charity Reuben
Francisca Ordega
3) KOCIN SHEKARA NAMIJI
Kennedy Boboye
Abdu Maikaba
Fidelis Ilechukwu
4) KOCIYAR SHEKARA MACE
Whyte Ogbonna
Edwin Okon
Ann Chiejine
5) MATASHIN DAN WASAN SHEKARA NAMIJI
Stephen Odey
Nura Mohammed
Ikouwem Udoh
6) MATASHIYAR YAR WASAN SHEKARA MACE
Rasheedat Ajibade
Anam Imo
Gift Monday
7) FITACCIYAR KUNGIYAR SHEKARA
Plateau United
Akwa United
MFM FC
Rivers Angels
Nasarawa Amazons
Ibom Angels
8) KWALLO MAFI KAYATARWA DA AKA ZURA A RAGA
Sikiru Olatunbosun (MFM v Rangers)
Shedrack Asiegbu (Abia Warriors v Plateau United)
Oche Salifu (Remo Stars v El Kanemi)
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu