Isa ga babban shafi
Wasanni

Kotu ta dage sauraron shari'ar 'yan wasan motsa jiki na Rasha

Kotun sauraron kararrakin da suka shafi wasanni ta dage shari’ar da ake dakon ta yanke hukunci kan yiwuwar shigar masu horarwa da kuma ‘yan wasan motsa jikin Rasha 47, gasar Olympics ta kankara da Korea ta Kudu zata karbi bakunci.

Wasu daga cikin 'yan wasan motsa jiki na Rasha 28, da aka dagewa haramcin shiga wasani har abada, tare da Shugaban kasarsu Vladmir Putin.
Wasu daga cikin 'yan wasan motsa jiki na Rasha 28, da aka dagewa haramcin shiga wasani har abada, tare da Shugaban kasarsu Vladmir Putin. Reuters
Talla

A gobe Juma’a kotun zata yanke hukunci kan shari’ar, kuma a goben ne 9 ga watan Fabarairu za’a fara gasar Olympics din, zuwa ranar 25 ga watan.

Cikin ‘yan wasan motsa jikin na Rasha da lamarin ya shafa, akwai guda 28, wadanda a makon da ya gabata kotun sauraron kararrakin wasannin ta dage musu hukuncin haramta musu shiga wasannin har abada.

Rashawan 28, na ganin kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, ya tafka kuskuren cire su daga cikin ‘yan wasan da zasu fafata a gasar Olympics din da zata gudana a Pyeongchang na Korea ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.