Isa ga babban shafi
Wasanni

'Man Utd ce kulob mafi arziki'

Manchester United ta ci gaba da rike matsayinta na kungiyar da tafi samun kudadden shiga a jere cikin shekaru 2 inda ta zarta Real Madrid kamar yadda kamfanin Money League Deloitte ya rawaito.

'Yan wasan Manchester United
'Yan wasan Manchester United REUTERS/David Klein
Talla

Wannan shine karo na 10 da Utd ke kai wannan matsayi inda ta samu kudadden shiga euro milyan 676 tsakanin kakar 2016/17 kusan ban-banci euro miliyan 1.7 da Real Madrid ta Spain da ke na biyu.

A jiya Kuma Utd din ta tabbatar da saye Alexis Sanchez dan kasar Chile da ke bugawa Arsenal, inda zai kasance dan wasa mafi tsada a Frimiya.

Barcelona wacce Sanchez ya taba takawa leda, ita ce ta Uku a rahotannin da ke kasance na 21 da kamfanin na akantoci a Burtaniya ke tattarawa, sai Bayern Munich da ke na 4, Man City ta 5 Arsenal ta 6.

Idan aka tattara kudadden da kungiyoyi 20 da ke kan gaba wajen samun yawan kudadden shiga suka samu a kakar 2016/17 akwai ci gaba da aka samu na kashi 6 wanda ya tashi a kan euro biliyan 7.9 a cewar rahoton.

Nasaran da United ta samu a Europa ya taimakawa kudadden shiganta, Real Madrid kuma ta samu habbaka sakamakon cin kofin zakarun Turai da Kofin lig na Spain.

To sauran kungoyin da rahotan ya wallafa akwai

7.  Paris Saint-Germain 486.2

8.  Chelsea 428

9.  Liverpool 424.2

10. Juventus 405.7

11. Tottenham Hotspur 355.6

12. Borussia Dortmund 332.6

13. Atlético de Madrid 272.5

14.  Leicester City 271.1

15.  Internazionale 262.1

16. Schalke 04 230.2

17.West Ham United 213.3

18. Southampton 212.1

19.  Napoli 200.7

20. Everton 199.2

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.