Isa ga babban shafi
wasanni

PSG na fargaba kan lafiyar Mbappe

Kungiyar kwallon kafa ta PSG na cike da fargaba kan ko dan wasan ta Kylian Mbappe zai yi fama da mummunar jinya bayan wani taho mu gama da suka yi da mai tsaron ragar Lyon Anthony Lopes a zagayen farko na wasan da suka buga jiya inda Lyon din ta yi nasara kan PSG da ci 2 da 1.

Sai dai tuni dan wasan mai shekaru 19 ya aike da wani sakon Twitter ga masoyansa tare da cewa yana cikin koshin lafiya
Sai dai tuni dan wasan mai shekaru 19 ya aike da wani sakon Twitter ga masoyansa tare da cewa yana cikin koshin lafiya Reuters/Gonzalo Fuentes
Talla

A cewar kungiyar ta PSG bayan jerin gwaje-gwaje kan dan wasan wanda ya baje a filin kwallo jiya, an gano taruwar jini a kansa, sai dai babu tabbacin ko zai yi doguwar jinya ko akasin haka, yayinda yanzu haka aka umarceshi da komawa birnin Paris don hutawa.

Sanarwar da Club din na PSG ya fitar ya ce za kuma a kara wasu nau’ikan gwaje-gwaje a mako mai zuwa don tabbatar da lafiyar dan wasan, wanda dama a baya ya taba fuskantar makamanciyar matsalar.

Sai dai kuma wani sakon twitter da Mbappe mai shekaru 19 ya aikewa magoya bayansa, ya ce yana cikin koshin lafiya yanzu haka, kuma baya fatan faduwar ta sa ta razana su.

Wasan na jiya dai ya gudana ne ba tare da anga fuskar Neymar a fili ba wanda shima yanzu haka ke fama da jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.