Isa ga babban shafi
wasanni

Manchester City na shirin tsawaita kwantiragin Bruyne

Kungiyar kwallon kafa ta Manchster City ta shirya tabbatar da tsawaita kwantiragin dogon lokaci da dan was anta na tsakiya Kevin de Bruyne .

Kevin De Bruyne ya ci wa Manchester City kwallaye shida
Kevin De Bruyne ya ci wa Manchester City kwallaye shida Reuters / Darren Staples
Talla

Kwantiragin dan wasan mai shekaru 26 kuma dan asalin Belgium zai kawo karshe a shekerar 2021.

Bruyne wanda ya koma Manchester City daga Wolfsburg akan farshin Pam miliyan 55 na taka rawar gani a kungiyar, lamarin da ya sa ta ke ganin ya cancaci ta tsawaita ma sa kwantiraginsa har zuwa shekarar 2024 kamar yadda rahotanni ke cewa.

Dan wasa ya ci wa Manchester City kwallaye 6 a wasannin Premier, yayin da kuma ya taimaka a ka ci kwallaye 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.