Isa ga babban shafi
Wasanni

Sanchez na gaf da komawa Manchester United

Mai horar da Manchester United Jose Mourinho ya bayyana kwarin gwiwar dan wasan gaba na Arsenal Alexis Sanchez zai amince da sauya sheka zuwa kungiyar.

Dan wasan gaba na kungiyar Arsenal Alexis Sanchez.
Dan wasan gaba na kungiyar Arsenal Alexis Sanchez. Reuters / Carl Recine
Talla

Tun a makon da ya gabata ake dakon ganin tabbatar cinikin dan wasan tsakanin United da Arsenal kan euro miliyan 39.6.

Tuni dai dan wasan United da za’a yi ciko da shi a cinikin Sanchez wato Henrikh Mkhitaryan ya amince da komawa Arsenal.

Shi ma mai horar da Arsenal, Arsene Wenger, ya bada tabbacin cewa ana gaf da kammala cika yarjejeniyar saidawa Manchester United Alexis Sanchez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.