Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta tsawaita wa'adin yarjejeniyar mai horar da 'yan wasanta

Hukumar kula da kwallon kafa ta najeriya NFF, ta tsawaita wa’adin yarjejeniyar mai horar da ‘yan wasan Super Eagles Gernot Rohr.

Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Gernot Rohr.
Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Gernot Rohr. Reuters/Peter Cziborra Livepic
Talla

A ranar Larabar da ta gabata hukumar ta NFF ta gabatarwa Rohr bukatar ya ci gaba da jagorantar ‘yan wasan tsawon shekaru 2, wadda ya amince da ita.

A shekarar 2016, Rohr ya karbi ragamar horar da ‘yan wasan na Najeriya, bayan da suka gaza samun cancantar zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika da ta gudana a shekarar 2017.

A karkashin sabon mai Gernot Rohr Najeriya ta zama kasa ta farko, da ta samu cancantar halartar gasar cin kofin duniya da za’a yi cikin wannan shekara a kasar Rasha.

Zalika a karkashin jagorancinsa, Najeriya ta lallasa kasar Argentina da kwallaye 4-2, a wasan sada zumuncin da suka buga a cikin watan Nuwamba, na shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.