Iheanacho ya kafa tarihi a alkalancin bidiyo a Ingila
Dan wasan Najeriya da ke taka leda a Leicester City, Kelechi Iheanacho ya zama dan wasa na farko da ya zura kwallon da fasahar bidiyon alkalanci ta amince da ita a Ingila.
Wallafawa ranar:
An fara amfani da wannan fasahar ce don taimaka wa alakalin wasa wajen yanke hukunci, yayin da Iheanacho ya fara zura kwallon farko da bidiyon ya amince da ita a fafatawar da kungiyarsa ta casa Fleetwood da ci 2-0 a a gasar FA a jiya Talata.
A karo na uku kenan da ake gwajin wannan fasahar a Ingila, in da aka yi amfani da ita a fafatawar da Brighton ta yi da Crystal Palace da kuma karawar da Chelsea ta yi da Arsenal duk a cikin wannan watan na Janairu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu