Isa ga babban shafi
Wasanni

Sanchez na dab da sanin makomarsa -Arsene Wenger

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya ce nan gaba kadan dan wasa gaba na Kungiyar Alex Sanchez zai san makomarsa, amma ya rage ga dan wasan ya zabi inda hankalinsa zai fi kwanciya.

Alex Sanches bayan zura kwallo a raga yayin wasansu da Manchester City a gasar cin kofin FA.
Alex Sanches bayan zura kwallo a raga yayin wasansu da Manchester City a gasar cin kofin FA. Reuters / Carl Recine
Talla

Wenger na wannan bayanai ne bayan rashin nasarar da suka yi a hannun Bournemouth da ci biyu da daya a wasannin Primier wanda Sanchez bai halarta ba.

Sanchez dan kasar Chile mai shekaru 29 hankalinsa yafi karkata zuwa Manchester City amma kuma kawo yanzu Manchester United ta amsa bukatar Arsenal kan cinikin dan wasan.

Kungiyoyin biyu dukkaninsu sun nuna sha’awar sayen dan wasan a ranar karshe ta kasuwar cinikayyar ‘yan wasa a waccan kaka ta watan Agusta, amma kuma ba’a kai ga kammala ciniki ba har aka rufe kasuwar

Arsenal dai na bukatar yuro miliyan 39 don sayar da dan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.