Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo zai bar Madrid kowanne lokaci daga yanzu

Zakaran kwallon kafa na Duniya Cristiano Ronaldo da ke taka leda a Real Madrid ya ce akwai yiwuwar ya sauya sheka a cikin wannan kaka sakamakon wasu matsaloli da yake fuskanta tsakaninsa da hukumomin kungiyar.

Ko da yake Ronaldo bai bayyana Klub din da ya ke son komawa ba, amma akwai raderadin dan wasan zai koma taka leda a Manchester United.
Ko da yake Ronaldo bai bayyana Klub din da ya ke son komawa ba, amma akwai raderadin dan wasan zai koma taka leda a Manchester United. REUTERS/Sergio Perez
Talla

Ronaldo dan Portugal mai shekaru 32 ya ce tun ba yanzu ba masu sharhi kan al’amuran wasanni ke shelar cewa zai sauya sheka zuwa wata kungiya daban, inda ya ce tabbas batun na gab da zama gaskiya.

A cewar Ronaldo dalilin sauya shekar tasa baya rasa nasaba da rashin biyansa kudaden da ya kamata a kungiyar, duk da cewa dai wasu na ganin hakan baya rasa nasaba da rashin tabuka abin kirki a wannan kaka.

Duk da cewa Ronaldo bai bayyana kungiyar da ya ke son komawa ba, amma akwai rahotanni da ke cewa dan wasan na shirye-shiryen komawa tsohon klub dinsa wato Manchester United.

Kafin yanzu dai Ronaldo ya sha yin korafe-korafe kan halin da yake ciki na rashin jin dadi a Real Madrid, batun da ke nuna alamun yana gab da barin kungiyar.

A waccan kaka anyi zargin cewa Ronaldo na shirye-shiryen komawa PSG, sai dai bayan sayen Neymar da klub din ya yi kan Yuro miliyan 200, dan wasan ya sauya tunani zuwa wata kungiya ta daban.

Bayan sabunta kwantiraginsa a shekarar 2016, Realmadrid na biyan Ronaldo Yuro milyan 21 kowacce kaka, kasa da kudin da Bercelona ke biyan Messi.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.