Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyar Evergrande ta yi tayin euro miliyan 70 kan Aubameyang

Kungiyar Guangzhou Evergrande ta kasar China ta fara zawarcin dan wasan gaba na kungiyar Borussia Dortmund Pierre Emerick Aubameyang.

dan wasan gaba na kungiyar Borussia Dortmund Pierre-Emerick Aubameyang.
dan wasan gaba na kungiyar Borussia Dortmund Pierre-Emerick Aubameyang. Wolfgang Rattay / Reuters
Talla

Idan har Aubameyang ya amince da tayin sauya shekar zuwa China, zai kafa tarihin zama daya daga cikin manyan ‘yan wasan da zasu fi daukar albashi, zalika mafi tsada da wata kungiyar daga kasar China ta saya da daraja.

Kungiyar ta Evergrande, wadda Fabio Cannavaro ke bugawa wasa ta shafe watanni biyu tana tattaunawa tsakaninta da wakilan Aubameyang.

Guangzhou ta yi tayin sayan da wasan kan euro miliyan 70, inda zata rika biyansa albashin euro miliyan 18 a shekarawato zata rika biyansa euro dubu 345,000 kenan a duk mako.

Sai dai har zuwa yanzu kungiyar ta Guangzhou Evergrande bata ce komai ba dangane da wannan rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.