Isa ga babban shafi

Ban dasa bam da niyyar hallaka 'yan wasan Dortmund ba - Sergie

Matashin da aka gurfanar a gaban wata kotu a Jamus, bisa zarginsa da sa wa motar ‘yan wasan kungiyar Borussia Dortmund bam, ya amsa laifinsa.

Sergej W, matashin da ya amsa laifin dasa bam a hanyar da motar da 'yan wasan kungiyar Borussia Dortmund zata wuce. 8, Janairu, 2018.
Sergej W, matashin da ya amsa laifin dasa bam a hanyar da motar da 'yan wasan kungiyar Borussia Dortmund zata wuce. 8, Janairu, 2018. REUTERS/Bernd Thissen/POOL
Talla

Matashin mai shekaru 28 da aka saya sunansa da Sergie W, wanda kuma Bajamushe ne amma dan asalin Rasha, ya shaidawa kotun da ke Dortmund cewa, bai yi niyyar hallaka kowa ba a harin da ya kai wa motar ‘yan wasan.

An kame Sergei W ne a birnin Rottenburg da ke kudancin Jamus, kwanaki goma bayan kai harin.

Daga bisani ne kuma masu bincike suka gano cewa ya siga wata gasar caca ce, inda ya yi da’awar cewa muddin ya kai harin hannayen jarin kungiyar ta Dottmund zasu fadi a kasuwar hada-hadar kasar Jamus, wanda kai tsaye hakan zai bashi damar samun kazamar riba.

Koda a ce hannun jarin kungiyar ta Dortmund ya fadi ne da euro daya, ana sa ran Sergie W, zai samu ribar akalla euro miliyan 500,000 daga gasar cacar.

Harin dai ya raunata dan wasan baya na kungiyar ta Dortmund Marc Bartra, yayinda karar tarwatsewar Bam din ya kurumtar da wani jami’in dan sanda.

Harin ya auku yayin da ‘yan wasan Dortmund ke kan hanyar zuwa buga wasan kwata final tsakaninsu da Monaco cikin watan Afrilu, a gasar zakarun turai ta shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.