Isa ga babban shafi
Wasanni

CAF ta soke kyautar gwarzon 'yan wasa da ke kungiyoyin Afrika

Hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, ta soke kyautar gwarzon dan wasan nahiyar da take bai wa ‘yan wasan da ke bugawa kungiyoyin gida sabanin na nahiyar turai.

Dan wasan Najeriya da ke bugawa kungiyar Al-Ahly wasa, Junior Ajayi a lokacin da ya zura kwallo ta biyu a ragar kungiyar Wydad Casablanca a Masar..
Dan wasan Najeriya da ke bugawa kungiyar Al-Ahly wasa, Junior Ajayi a lokacin da ya zura kwallo ta biyu a ragar kungiyar Wydad Casablanca a Masar.. rihabnews.com
Talla

CAF ta dauki matakin ne a ranar Laraba da ta gabata, kwana guda, kafin ta yi bikin bayar da kyaututtuka a jiya Alhamis.

Shugaban hukumar Ahmad Ahmad, ya ce an dauki matakin ne kasancewar saboda kaucewa nuna banbanci akan matakin kwarewar ‘yan wasan nahiyar Afrika, dan haka a cewar shugaban za'a rika bada kyautar ne bisa cancantar kwazo da kwarewar dan wasa, ba tare da la'akarin nahiyar da yake wasa ba.

Kafin daukar matakin soke bada kyautar, dan wasan Najeriya Junior Ajayi ne ke kan gaba a tsakanin takwarorinsa da ke wasanninsu a gida, wanda ake sa ran zai lashe kyautar gwarzon dan wasan na nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.